Tsutsar masara /Spodoptera

Tsutsar masara da ake cema da turanci : Spodoptera frugiperda .

A shekara ta 2016, wata sabuwar tsutsa ta bayana a kasar africa,wanan tsutsar ta mamaye kasashen africa da dama kamar su nigeria,benin,togo,africa ta kudu da sauran su ; tsutsar masara spodoptera frugiperda tayi banna sosai a cikin gonankan masara.
Wannan tsutsar masara ana ce mata spodoptera frugiperda a turance,an ganota ne a karon farko jikin masara a garin torrodi da maradi shekara ta 2016 ;tun daga wanan lokaci sai ta bazu a dukan fadin kasa.

Abun al’ajabi wanan tsutsar bata tsaya ga masara kadai ba, a lokacin daminar bara a garin maradi da torodi ta apkama gonankan hatsi inda tayi bana sosai ;wanan tsutsa dai babbar matsala ce ga hatsi da dawa, ya kamata manoma su nemi saninta don su yaketa.

Télécharger la note Tsutsar masara, 4 pages, 502 Ko.

Documents joints