Yaki da murzuna

Yaki da murzuna ba tare da zuba maganin miyagun kwari, abune ne mai yiwa !

Manoman kasar Nijar na cigaba da fuskantar barazar muguwar tsutsar nan mai cinye kwayar gero wanda ake cema MURZUNA.

MURZUNA na apkama hatsi ne a lokacin da ya fidda kaye kuma manomi ke zaton cewa zai samun samu hatsi sosai ; nan da nan sai ta cinye kwayar geron idan ba’a dauki mataki ba da wuri sai ma ta ciye hasti ga baki daya.

Lokacin da murzuna ta bayana a cikin wani yanki ta kan iya mamaye ilahirin gonankan dake wajan sanan kuma magani baya tasiri a kanta. Aman akoye wata hanyar yaki da wanan tsutsar MURZUNA.

Zamu gabatar muku da husa’ar nan ta renon diyan rina wanda turawa ke cema HABROBRACON.

Rina wani dan karamin zanzaro ne mai kama da zuma kuma ya shahara wajan yaki da MURZUNA saboda diyan ta ke cinye tsutsar.

Karamcin rinar da ake fama dashi baya iya kashe tsutsar,gata kuma da yawan aihuwa.

Saboda haka dole sai manoma sun dage wajan kiwon rinar dan tayi yawa suji dadin yaki da stustar (MURZUNA).

Wasu kungiyoyin manoma na TERA da DANTCHANDU a cikin jahar Tillaberi sun kware wajan kiwon na rinar. Wanan kungiyoyin manoman sun samu horo ne na musaman kuma suna cigaba da sayar ma wasu manoma dan su rinka kare gonankansu ; wanan husa’ar ta kungiyar manoma HAREYBANE ta Tera, daya daga cikin menbobin babbar kungiyar MOORIBEN ce zamu bayana muku a yau.

Télécharger la fiche Haoussa, 4 pages, 388 Ko.

Documents joints