Tabarbarewar iri shuka

Tabarbarewar iri shuka

Cikin rahotanni da dama da suka gabata ana zancen tabarbarewar irin shuka na nau’in albasar Galmi.

RECA Info ta tambayi Dr Moumouni DAGNA na Ma’aikatar Ministan da ke kula da noma da kiwo don ya kawo haske ga wannan kalma da kuma illarta.

Ita dai tabarbarewar nau’i, wanda za a iya kwatantawa da zaizayar halitta, na wakana musamman ga irin shuka da aka zaba kuma aka kebe da ke gamuwa da gushewar yanayin kamanninsa wanda saboda shi ne aka zabe shi don adanawa.

A misali, game da irin albasa, muhimman abubuwan da ke sa a zabi irin shuka, su ne : ba da amfani, tsawon kwanakin da yake dauka wajen ba da amfanin, yanayin adano, siffa, launi, da gaugawar nuna, rishin ba da tsaba da bununi a shekarar farko, dandano, rikon kamanninsa a yanayin bushewa, kare kai daga cututtuka, da dai sauransu.Ma’anar nau’i ya danganta da yanayi daban daban da ke bayyana a zahiri, da kamanni daya da kuma rishin sauya kamannin nan a tsawon lokaci.

A bangaren albasar Galmi ko, an zana yanayin kamanninta cikin kundin da ke kumshe da irin nau’i daban daban na kasar Nijar da na Afirka ta Yamma (a duba cikin shayi). Wadannan alamomi na bambanta albasar Galmi da sauran nau’o’in albasa. Ana cewa da ire-iren albasa na da nau’i daya idan suna da kamanni kamar haka : launi iri daya, siffa iri daya, d.s.

A karshe, ana cewa wannan nau’in muhimmi ne idan an tabbatar yanayin kamanninsa ba su canzawa a kowane hali na ba da amfani da kuma yaduwarsu.
Haka wajen sharuddan tabbatar da nau’i daya sai an samu ire-iren yanayin da aka tsaida wa irin shuka.

A lokacin noma, wasu daga cikin alamomin da aka tabbatar da su ga nau’in shuka za su soma gushewa, misali launinta, siffarta, da kuma nunar amfaninta.
A wannan lokacin ne za a fara maganar tabarbarewar nau’in.
Dalili ke nan ake samu a wajen wasu manoman albasar Galmi ire-iren nau’o’i masu siffofi daban daban da hade-haden launi.

Don mi ake samun wannan gushewar kai-a-kai ?
Albasa dai shuka ce mai dauke da bununi, ke nan tabarbarewar nau’in nata na kasancewa ta hanyar rishin daukan matakai kan yada bununin nan nata. Ke nan mizanin yaduwar albasar na kasancewa daga 0 zuwa 50 bisa dari.

A takaice dai, fiye da rabin dashen da aka yi, wato dashen shukar tamata na yaduwa da taimakon bununin dashen shuka jinsin namiji, a wani fannin ma da taimakon wasu kwari.

Tsabar da aka noma a gonar albasa na da dangantaka da albasar da aka dasa da kuma albasar da makwabta suka dasa. Idan ko ya kasance nau’in nasu ba guda ba ne, ke nan irin shukar na da hadi.

Bayan an shuka wannan iri, albasar da za a noma za ta samu alamu daban da wadanda aka sani na wannan nau’in, dalili ke nan suna iya tabarbarewa a tsawon lokaci.

Tabarbarewar irin shuka A nan Nijar, a fuskar noman albasa (inda ba a cika yin amfani da zababben iri shuka), ke nan tabarbarewar nau’i abu ne mai wakana, wanda za a lura da shi a zahiri a kasuwanni, inda za a lura da zaizayar launinsa, da ta siffarsa har ma da canzawar dandanonsa musamman a albasar Galmi, game da alamomin da aka sani wanda take da shi. Saboda da haka, ake ba da shawarar yin amfani kai-a-kai da zababben irin shuka don samun cikakken amfani na gari mai alamomin da mutane suke bukata.

Dalili ke nan binciken da ake zartarwa (ma’aikatar INRAN) shi ne don a tsabtace nau’in irin da ake shukawa a cikin gonakin da ma’aikatar ke kula da su. Binciken za ya samo iri mai kyau mai nuna alamomi na nau’in albasar Galmi. A haka ne ma’aikatar INRAN ke samar ma gon kinta na Konni da na Maradi irin shuka mai kyau na nau’in albasar Galmi.

Bayan haka, duk manomin da ya lura da albasar da ya noma ba ta yi kama da nau’in da ya kamata ya noma, to ya cancanta ya je ya nemo iri mai kyau.

Kungiyar nan ta manoma (FCMN Niya) ta horar da wasu manoman irin shuka mai kyau a cikin kungiyoyi da suka kai guda goma a cikin kasar Nijar (don karin bayani a karanta hirar da aka yi da Malam Ali Amadou, daya daga cikin manoman irin shuka).

Su ko wadannan irin shuka na samuwa daga tsabar da INRAN ke nomawa a gonakinta na musamman, wadanda suke samun kariya ta muasamman game da sauran noman albasa na makwabta don gudun hadi. Don a lokacin noman, ana kula da gonakin nan inda ake fitar da duk wata albasa da ba ta dace ba da alamomi ko yanayin albasar Galmi.

Idan aka fitar da tsabar nan sai a gyara ta da kyau yanda za ta rike mizaninta na tsiro. A karkarar Madawa, ANFO na horar da manoman irin shuka musamman don samar da irin albasa mai kyau.
A karshe, ana iya cewa tabarbarewar nau’i ba ya alaka da yanayin tsiro na irin shuka. Abu ne biyu da suka bambata.

Yiwiwar tsiron irin da aka shuka ya danganta da kulawar da aka tanada wajen noman tsabar (dibar ta lokacin da ta nuna, shanya ta a cikin inwa, kakkabar ta a hankali, da kula da ita wajen ajiya).

Amma a nan ya cancanta a amince da aikin da manoma na musamman ke yi don samar da iri mai kyau. Kamar Malam Ali Amadou da ya san aikinsa.


Tsawon kwanakin shuka zuwa nuna : kwana 120 zuwa 130
Siffar kullutu : mulmulalle da fadi a sama
Launin fatar : ja da shudi
Samun amfanin : tan 30-40 a kowace eka
Jure wa ajiya : Mai kyau
Sauran alamu : Mai rauni ga Fusarium, da
Aspergillus, da Xanthomonas da kuma cutar
sayun shuka ; Mai jurewa cutar Nématodes à
Galle ;
Mai saurin nuna ;
Mai dandano zazzafa yadda mutane ke bukata.

Documents joints