Takin fosfor

An yi rukuni don ni’imantar da kasar noma a Nijar : shi ne fosfor

A Nijar, yawancin kasar noma na darashin isasshen rukuni na takin fosfor.Ko da yake shi wannan rukuninyana kawo nasa taimako wajen rayayanayin shuka da yawaita samunisasshen amfanin noma. Shi dai fosfor,dan karamin rukuni ne a dimbin rukunai da shuka ke amfani da su donrayuwarta. Su dai shuke-shuke natatso wannan rukunin daga kasarnoma ko kuma ta hanyar taki iri-irida ake zuba masu.

A kasuwanninmu ana samun taki mai dauke da gishirin fosfor kamar haka :
- Babban fosfat mai rukuni daya (SSP : 18% P, 18-21 CaO, 12% S) ;
- Fosfat mai diyamoniyum (DAP : 18% N, 46% P) ;
- Babban fosfat mai rukuni uku (TSP : 45% P, 3-14% CaO, 1% S)
- Fosfat na Tahoua (PNT : 27% P) a Niger.
Ana kuma iya ba shuka gishirin fosfat ta hanyar hada azot da potassiumkamar misali takin NPK (15-15-15).Yawancin taki mai dauke da fosfat ba ya saurin narkewa, da sannu sannu yake sakin gishirin fosfat, dalili ke nan yake dadewa cikin kasa yana aiki (misali shekara 3). Don karfafa shi, yana da kyau a yi amfani da shi a taki da ake binnewa. A nan za a yada shi da kyau kuma a tura shi can cikin kasa.
Amma a yanzu, an same shi na ruwa, wannan za ya taimaka matuka ta yadda sayyun shuka za su same shi nan take. Yin amfani da fosfat yana kasancewa da yanayin abin da aka shuka da kuma matsayin tafiyar da ci-gaban shuka.
A misali bangaren hatsi, yana bukatar fasfor mai dimbin yawa tun daga tashinsa har ya zuwa bununi. Za a yi amfani da fosfor mai rukuni uku har kilo 50 a kowace eka, ko kuma kilo 100 a eka na fosfat mai rukuni daya. A bangaren shinkafa kuwa, za a yi amfani da fosfat na Tahoua (PNT) kilo 300 a eka a kowace shekara a tsawon noma biyu.

A nan kasar Nijar, akwai hanyoyi da dama da ake amfani da takin fosfat.
Ana amfani da taki TSP inda a kowace eka ana sa kilo 50, ko kuma taki SSP inda za a sa a kowace eka kilo 100 da hadin takin Ure kilo 50 a eka.
Ko da yake yadda talauci ya yi kanta a manoman kauye da rashin isasshen ruwan sama da ake samu, sun sa mun dauki hanyoyi marar tsada ta yin amfani da taki mai arha yanda ba za ya kawo wani aibi ba ko da an samu karancin ruwa, wato yin amfani da taki DAP kadan bisa hatsi kamar kilo 20 a eka da hadin Ure kilo 10 a eka yayin da hatsi ya hau kara. A noman lambu ko, hadadden takin nan NPK an fi amfani da shi wajen takin binne da na barbadawa.
Misali wajen yin amfani da NPK (15-15-15)
ga yadda za a yi :
A takin binne :
- Kilo 5 a 100 m2 a noman karoti da tugande ;
- Kilo 2,5 a 100 m2 a ganye (salati da shu) da dankalin turawa da albasa
- Kilo 4 a 100 m2 a noman malo, gurji da tumatur.
A takin barbadawa :
- Kilo 6 a 100 m2 a noman karoti, gurji, malo da albasa ;
- Kilo 8 a 100 m2 a noman tugande da tumatur ;
- Kilo 6,5 a 100 m2 a noman ganye (salati da shu) ;
- Kilo 7,5 a 100 m2 a noman obarjin da irin su kabewa
- Kilo 5 kg a m2 a noman dankalin turawa.

BINCIKE : Samuwar isasshen taki ga manoman Nijar noma.

Ita dai wannan ma’aikata CA na kula da duk wani taimako na kyautata noma da kasashen waje za su ba Nijar, tana kuma sayen kayan noma daga manyan kampanoni na duniya kamar su (kayan noma, injina, magunguna, taki, iri na shuka, da sauran tarkacen kyautata noma) don ita kuma ta sayar wa manoma a duk cikin fadin kasar Nijar a kan farashi guda.
Bayan wannan, ma’aikatar CA na samun kyautar dussa da ta kai kashi 50 zuwa 70 bisa 100, sauran sai ma’aikatar ta saya da kudinta a wajen manyan kampanonin duniya.
Wadanne matsaloli ne kungiyoyin manoma ke haduwa da su wajen ma’aikatar Centrale d’Approvisionnement (CA) ?

A wannan ma’aikatar CA, kungiyoyin manoma na kuka kwarai wajen rashin samun aiken takin da suka saya a ma’aikatar a cikin lokaci, dalili ko, rashin sa a ma’ajiyar ta ma’aikata inda kasashen duniya da ke ba su takin suna yi masu alkawari ba da cikawa ba.
Wata kankanuwar matsala da manoma ke gamuwa da ita shi ne matakan biyan kudi mararan inda su manoman ba su da shi a farkon aikin noman don sayen kayan noma.
Kungiyoyin manoma na jinini da cewa ba a shawartar su wajen daukan duk wata niyya game da tsaida farashi ko yin odar kayan noma. Hakika matsaloli na da mahimmanci da yawan gaske.
Wadanne shawarwari kungiyoyin za su kawo don cimma matsalolin ?
A nan ma kungiyoyin manoma sun yarda su amwa wa RECA Info :
Don magance wadannan matsaloli, ya wajaba manoman su hada kai don su samu takinsu ta hanyar oda da gungun jama’a za su yi a kungiyoyin. Sun kawo shawarar da ya kasance suna cikin kwamiti da ke kula da kudaden ma’aikatar CA domin ta haka kadai ne za a kula da bukatocinsu musamman abin da ya shafi oda da tsaida farashin taki.
Bayan wannan, suna fatar su samu goyon bayan abokan arziki don kafa shaguna na sayar da kayan noma yadda za su rinka samun takin zamani kai a kai ga manoma.
Zababbun hanyoyin da suka dace don magance wadannan matsaloli, kungiyoyin na da niyyar sabunta ni’imar kasar noma ta hanyar aiki da yanayin wuri (wato dasa itace da kula da su don su samar wa kasar noma sinadaran da za su taimaka wa shuka) da kuma (ni’imantar da kasar noma ta hanyar zuba mata taki na ganye da tsumamar ganyayyaki). Ita ce hanya mafi sauki ga duk manomi ta ni’imantar da kasar noma. Suna kuma da niyyar daukaka hanyar yin amfani da fosfat na Tahoua (PNT).
Amma hanya mafi sauki don cimma matsalolin samun kayan noma a cewar wadannan kungiyoyi, ita ce kirkiro da wata ma’aikatar gwamnati da ke kula da kasuwancin wadannan kayayyaki, inda su ma kungiyoyin za su zuba hannayen jari kuma ya kasance suna cikin kwamitin
tafiyar da ma’aikatar.
A karshe, a hakikance kafuwar banki mai kula da noma don ba manoma dammar daukan bashi.

Documents joints