Sabuwar kafaffar doka kan kiwo
Kudiri mai lamba 2010-029 na 20 ga watanbiyar (mai) 2010 da ya shafi kiwo, ya tabbata.
Wannan shirin doka ya tabbata ta hanyar shirya tarurruka da aka yi da halartar kungiyoyin karkara na duka jahohi, inda yawan tarurrukan da ya kai fiye da dari.
Ga wasu muhimman matakai na wannan kafaffar dokar kan kiwo da ke nuna ci-gaban makiyaya, kamar misali :
Ayar doka ta 3 : Tana nuna cewa " walawa tana daya daga cikin tsarin shari’ar da
makiyaya da masu sana’ar kiwo suka samu don yin amfani da ita". Hakki ne da gwamnati da kananan hukumomi suka amince da shi kuma suke kare shi. Ita dai wannan walawar, doka ta tabbatar da hanya ce ta hakika mai jurewa wajen tafiyar da ayyukan kiwo.
Aya ta 5 : Tana zance kan hanin mutum ya mallaki musamman wurare da suka zamanto na kiwo ne mallakar gwamnati ko kananan hukumomi. A karkashin mataki na 2 na wannan dokar, an kiyasta cewa " a hakika ba a yarda ba da duk wata sasantawa ko ragowa idan dai har za su kawo wata danniya a fuskar walawar
makiyayan da dabbobinsu da za su rasa samun albarkar kiwo ".
Aya ta 12 : Hakkin mallaka wato hakki ne na zama a wuri, da morewa, da kuma kula da wurin ga makiyaya game da yankin wuraren da suke daure dabbobinsu. Ayar na kawo haske wajen amfani da abubuwan da Allah ya hore mana, haka ta tsaida matakan da za su kayyade hakkin mutanen da za su amfana ta hanyar
doka da al’adu da tabi’o’in wurin.
Aya ta 17 : Ita wannan ayar na zance kan matakan kula da riyojin da gwamnati ta tanada don kiwo. " Kula da duk wata rijiya da aka gina don kiwo tana karkashin yankin magajin gari, wanda kuma shi ne madugun aikin. Haka ma’aikatar magajin gari na iya kiran duk wani komiti ko wata ma’aikata mai kula da sha’anin
ruwa a kan wata yarjejeniya ta kula da tafiyar da ayyukan tsakanin mutanen da gwamnati ".
Aya ta 59 : Wannan ayar na tabbatar da kulawar wurare masu dandanon gishiri a karkashin ma’aikatar magajin gari da yancin amsar tara idan ta shafi kasuwancin wuraren. Amma karamar hukumar na da yancin hana duk wata haraka da ke tauye duk wani biyan bukata na makiyayan.
La note complète est jointe.