noman rani a sauЌaЌe

Kundin noman rani a sauЌaЌe a jahar Damagaran

Manuel d’irrigation Goutte à Goutte dans la Région de Zinder

Gabatarwa

Sama da kashi tamanin da biyar cikin ďari na al’umar Nijar na raye cikin karkara, kuma sun dogara ne a kan noma. Rishin saukar ruwan sama a kai a kai na kawo cikas ga albarkatun noma. Bayan hakanan, Ќaramcin tabkuna basu bada damar bunЌasa noman rani. Dangance da haka,cibiyar ta kungiyar SOS SAHEL me bincike bisa tattalin albarkatun karkara, tare da haďin gwiwa babbar ma’aikatar gidan gona ta jahar damagaran sun samo sabuwardubara ta noman rani a sauЌaЌe, da suka fara gudanar daaikin a shekarar ta dubu biyu da shidda (2006). Wannandubarar nada gurin ta yaЌi tamowa, kuma da talauci a cikin iyali.

Wannan gurin ya dace da siyasar Nijar ta bunЌasa karkara, wanda aka rubuta a cikin kundi na hikimomin bunЌasa karkara. Mahimancin riga kahi abinci,yin tattali me ďaurewa na albarkatun karkara dan kare rayuwar al’uma daga matsala, yaЌi wajen Ќaramcin abinci bisa hanyar bunЌasa noman rani.

Noman rani a sauЌaЌe dubara ce mai sauЌi wadda ake saye da arha, kuma ba ta da Бannar ruwa. Wajen sama da dubu shidda (6.000) masu aikin garka na cikin gungun al’uma mai raunin rayuwa na garuruwa ďari ukku da sattin da bakwai (367) na jahar damagaran suna amfani da wannan hikima.

Dalilin sakamakon mai kyau da sabuwar hikimar ta bada a cikin jahar damagaran, ya sa muka ga ya dace noman rani a sauЌaЌe ya yaďu cikin sauran jahohi na Nijar, da kuma sauran Ќasashe na yankin sahel.

Télécharger le manuel d’irrigation Goute à Goute en version haoussa , 19 pages, 504 Ko

Documents joints