Zogalagandi (windi bundu)

Zogalagandi, tambaya mai yawa, samuwar ta kalilan

Zogalagandi ko zogala ko zogale ko kuma tamaka ko yal (yar) makka yanda ake
kiran ta a kasar hausa, wadda Zabarmawa ke ce ma windi bundu. A cikin wannan watan na satumba, za a ga manyan motoci shake da buhunnan zogala inda mata yan kasuwa ke rububinta a kasuwannin birnin Niamey. Muna cikin lokacin damana, wato daidai lokacin noman ita wannan zogala. Su dai mazamna
birnin Niamey sun shahara wajen cin wannan ganye na zogala mai kumshe da
bitamin, da karhe, da sinadirori da sauran furotoyin. In an duba ko suna da gaskiya, domin garam 100 na danyen ganyen zogala na samar da furotoyin kin da kwai daya ke badawa, haka daidai da sinadirorin kalsiyom da za a samu a finjalin

kan kudi cfa 400 a karamar kasuwar Niamey, wanda kashin ya yi daidai da
nauyin 2,5 kg a misali. Wannan ko za ya yi daidai da kwayaye da finjalan madara
masu dinbin yawa.
Gyaran ta da kyau Kamar sauran ire-iren cimaka, matsalar daya ce ta wajen dahuwar ta inda take son kulawa don kar a rasa sinadirorin da ta kumsa na gina jiki, kamar su bitamin da ke lalacewa lokacin dahuwarta. Ana ba da shawarar a yi saurin cin ganyen zogala bayan an tsigo shi, sannan wajen dahuwar kar ta dau lokaci mai tsawo.

Yana kuma da kyau a adana ruwan nan da aka dafa ta (ruwa ko miya) wato bayan
madara guda. Ko kuma daidai da yawan karhen da za a samu a tsagin nama. Idan
ko aka duba garam 100 na ganyen zogala ba shi da yawa. A karshen watan takwas (août) na 2010 ana saida kashin zogala a an dafa. Bayanan da aka samu na game da ruwan da aka dafa ta, suna da dadin sha ne. Yin kuma garin ta, wata hanya ce mai kyau don adana abubuwan da ta kumsa na gina jiki (ko da yake ana asararsu lokacin da aka shanya ta), ana iya yin anfani da wannan gari bayan an dafa abinci. Garin zogala na kumshe da furotoyin, bitamin, da sauran sinadirai,
wadanda ya kamata a yi anfani da su.

La note complète est jointe.

Documents joints